Wasu Jami’o’i Nijeriya sun sha alwashin taimaka wa daliban da aka kwasho daga kasar Sudan sakamakon yakin da ke ci gaba da kamari a kasar.
A wata sanarwar da hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) ta fitar a ranar Asabar, ta ce, Jami’o’i da dama ne suka nuna sha’awarsu na daukan daliban Nijeriya da aka dawo da su daga Sudan da suka hada da jami’ar Igbinedion, Okada, da ke jihar Edo, jami’ar Summit, Offa, jihar Kwara, da jami’ar American University, the Gambia da dai sauransu.
- Wane Ya Sabawa Ka’idojin Kasa Da Kasa?
- Bagudu Ya Gabatar Da Takardun Shaida A Kotun Sauraren Kararrakin Zabe A Kebbi
LEADERSHIP ta labarto cewa, hukumar samar da guraben karatu ta kasa (JAMB) ta yi alkawarin samar da dukkanin taimakon da suka dace wajen tabbatar da daliban Nijeriya da aka kwaso daga Sudan sun samu shiga cikin Jami’o’in da suke kasar domin cigaba da karatunsu.
Shugabar hukumar NIDCOM Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta yaba da kokarin da azamar jami’ar Igbinedion sa’ilin da ta amshi bakwancin mukaddashin shugaban jami’ar Farfesa Lawrence Ikechukwu Ezemonye a Abuja.
Abike ta nuna bukatar da ke akwai na cewa kowa ya bi ka’idar da JAMB ta gindaya domin kauce wa kowace irin matsala da ka iya biyo baya.
“Mun kasance tare da JAMB kuma JAMB din ta bayar da sharadi da ka’idojin da za a yi, na tabbatar kana sane don haka idan sun zo maka kana iya shigar da su, za mu bukaci wasika daga JAMB D’s ke tabbatar da cewa JAMB din ta bayar da izirin karatu, yin hakan zai sa a samu kauce wa matsalar fs mutum idan ya kammala karatu kada a zo a ce ba zai je hidimta wa kasa ba,” ta shaida.
Ta kuma shaida cewar zuwa yanzu ‘yan Nijeriya 2,371 ne aka kwaso daga Suzan zuwa Nan gida Nijeriya.