An kashe ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Sudan Shaden Gardood, a wata musayar wuta tsakanin ɓangarori biyun da ke faɗa da juna a ƙasar.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Misis Gardood ta rasa ranta ranar Juma’a a birnin Omdurman sakamakon faɗa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.
- Sudan: Jami’o’in Nijeriya Sun Sha Alwashin Bai Wa Daliban Da Aka Kwaso Guraben Karatu
- Sudan: Karin ‘Yan Nijeriya 126 Sun Iso Abuja
Mutuwar mawaƙiyar mai shekara 37 na zuwa ne kwana guda bayan ɓangarorin da ke rikici da juna sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen wahalar da fararen hula ke fuskanta.
A cikin watan Afrilu ne dai faɗa ya ɓarke a ƙasar tsakanin ɓangarorin biyu.
Gardood dai na zaune ne a al-Hashmab, inda dakarun RSF ke ƙaruwa a ‘yan kwanakin nan.
Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta an ga Gardoon na ɓuya tare da kiran ɗanta ya matsa daga kusa da taga domin kauce wa harsasai, yayin da ake ci gaba da luguden wuta a birnin.