Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce tun bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu shekaru 30 da suka gabata, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashe 5 na yankin tsakiyar Asiya, ya haifar da kwararan sakamako.
A cewar ma’aikatar, yawan cinikayya tsakanin Sin da kasashen 5 da suka hada da Kazakhstan da Kyrgyzstan da Tajikistan da Turkmenistan da Uzbekistan, ya karu zuwa dala biliyan 70.2 a shekarar 2022, daga dala biliyan 0.46 a 1992, lokacin da Sin ta kulla huldar diflomasiyya da su.
Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya ga Kyrgystan da Turkmenistan da Uzbekistan, kana ta biyu ga Kazakhstan, yayin da ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta 3 ga kasar Tajikistan.
Darajar cinikayya tsakanin bangarorin biyu ya samu karuwar kaso 40 daga shekara 1 da ta gabata. Haka kuma ta ci gaba da rike wannan kuzari, inda har ta kai ga samun karuwar kaso 22 a rubu’i na farko na bana.
Bugu da kari, tsarin cinikayya tsakaninsu ya yi ta ingantuwa cikin shekarun da suka gaba. A bara, kayayyakin amfanin gona da na bangarorin makamashi da ma’adinai da Sin ta shigo da su daga wadannan kasashe 5 ya karu da sama da kaso 50 a kan matakin da ya kasance shekara guda kafin wannan lokaci, yayin da yawan kayayyakin laturoni da injuna da kasashen suka saya daga kasar Sin ya karu da kaso 42. (Fa’iza Mustapha)