A yau Talata, mamban majalisar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen Sin Qin Gang ya gana da ministan kula da harkokin waje da na hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Saliyo David Francis a Beijing.
Qin Gang ya bayyana cewa, bangaren Sin yana yabawa bangaren Saliyo sosai wajen bin manufar kasar Sin daya tak, kuma ya tsaya tsayin daka kan adalci a kan hakkin dan Adam dake shafar jihar Xinjiang da sauransu.
Ya ce a bana ake cika shekaru goma da aiwatar da manufar kulla kyakkyawar dangantakar “nuna sahihanci da gaskiya da abota” da kasashen Afirka ta Shugaba Xi Jinping ya gabatar, don haka kamata ya yi bangarorin biyu su cimma muhimmiyar matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka tabbata tare, da ci gaba da tsayawa tsayin daka kan goyon bayan juna, da inganta hadin gwiwa, da kuma karfafa mu’ammala a kan harkokin yankunan kasa da kasa.
David Francis ya ce, dangantakar Saliyo da Sin tana da karfi sosai, kuma bangarorin biyu sun ci moriyar juna a fannoni da yawa. Ya ce bangaren Saliyo na dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninsa da Sin, kuma yana tsayawa tsayin daka kan bin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
Har ila yau, ya ce yana fatan karfafa hadin gwiwa tare da bangaren Sin a fannonin zuba jari a fannonin cinikayya da aikin noma da samar da manyan ababen more rayuwa da sauransu, ta yadda za a kawo alheri ga al’ummun kasashen biyu. (Safiyah Ma)