Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta kafa kwamitin binciken zagon kasa a zaben da ya gabata da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi na nuna adawa ga ‘yan takarar jam’iyyar a zaben da ya gabata.
Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na Jiha, Malam Yusuf Idris Gusau.
Shugaban Jam’iyyar na Jiha, Hon. Tukur Umar Danfulani ne ya jagoranci kaddamar da kwamitin a sakatariyar jam’iyyar ta jiha A yau Laraba, 17 ga Mayu, 2023
Shugaban jam’iyyar ya bukaci ‘yan kwamitin da su yi nazari sosai kan duk wasu zarge-zargen da ake yi wa kowa, ko da kuwa yana da ga cikin jigajigan jam’iyyar, don tabbatar da cewa yana da hannu wajen zagon kasa ga jam’iyyar tare da samar da matakan da za a dauka a kansa.
Tukur Dan Fulani ya bayyana cewa, tuni sakatariyar jam’iyyar ta jiha ke rike da kwafin koke-koke kan wasu ‘ya’yan Jamiyyar, ya ce kwamitin ya kamata ya gudanar da aikin nasa ba tare da tsoro ko son rai ba, sai don maslahar jam’iyyar.
Shugaban ya yabawa jarumai wadanda suka tsaya wa jam’iyyar da ‘yan takararta a rumfunan zabe bisa jajircewarsu duk da tursasawa da sojoji suka yimasu.kuma jam’iyyar za ta tabbatar da adalci ga dukkan mambobinta a kowane mataki.
A nasa Jawabin shugaban kwamitin Malam Yusuf Idris Gusau, ya godewa jam’iyyar da taga cancantar su ta zabosu wajan gudanar da wannan aikin.
Yusuf Gusau , ya yi alkawarin cewa kwamitin zai tabbatar da adalci wajan binciken wadanda ake zargin.
Mambobin kwamitin sun hada da, Yusuf Idris Gusau- A matsayin Shugaba, sai ,Barr Ibrahim Aliyu Ajiya, Dr. Mikailu Ibrahim Bara’u, Hon Nura Dahiru, Dr. Aminu Suleiman Yarkofoji, Alh kabiru Dankulu Bungudu, Hon. Faruku Musa Dosara, Alh Hamisu Habibu Kasuwar Daji, Barr. Junaidu Aminu, Hon. Anas Hamisu , a matsayin mambobi, Hon. Ibrahim Maaji- Secretary.