Kasar Zambia ta ce ta shirya jan hankalin karin Sinawa masu zuba jari, idan ta halarci taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na 3 dake karatowa.
Baje kolin karo na 3 mai taken “Ci gaba na bai daya, Makoma ta bai daya” zai gudana ne daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli a lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin. Baje kolin wanda aka fara gudanar da shi a shekarar 2019, katafaren dandali ne na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Ministan kula da kasuwanci da cinikayya da ma’asanantu na Zambia Chipoka Mulenga, ya bayyana cewa zai jagoranci tawagar ‘yan kasuwar kasarsa zuwa baje kolin, kuma kawo yanzu jimilar kamfanoni 21 sun bayyana sha’awar shiga tawagar. A cewarsa, ba za a bar su a baya ba, wajen cin gajiyar wannan dama da kasar Sin ta samarwa Afrika, da sauran kasashe.
Ministan ya kara da cewa, Zambia ta na matukar son sanin yadda Sin ta samu nasarori a fannin raya kasuwanci. (Fa’iza Mustapha)