• Leadership Hausa
Tuesday, December 5, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bani Da Wani Gida A Kasar Waje -Buhari

by Abubakar Abba
7 months ago
in Manyan Labarai
0
Ina Neman Gafarar ‘Yan Nijeriya Idan Na Muku Ba Dai-dai Ba —Buhari
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, bai mallaki wani gida a kasar waje ba.

Buhari ya sanar da hakan ne, a lokacin da ya karbi wasikun kama aiki na babban kwamishina da aka turo Nijeriya daga Landan, Richard Hugh Montgomery da takwaransa ba Sri-Lanka Velupillai Kananathan.

  • Shugaban Sashen Fassara Na Leadership Hausa, Malam Sabo Ahmad Ya Rasu
  • Bai Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Bi Sahun Ta Buhari Ba —Shugaban EYN

Shugaban wanda ya karbi wasikun nasu a yau Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce, ya kuma sanar da hakan ga Sarki Charles na III a lokacin wata ganawa da suka yi bayan da Charles ya tambaye shi, cewa ko yana da gida a Landan.

A cewarsa, “A ganawar da na yi da Sarki Charles na III, ya yi min tambayoyi masu ma’ana, inda daga ciki ya tambaye ni, ko ina da gida a Landan, ni kuma na mayar masa da amsa cewa, ban da gida ko da kafa daya, a wajen Nijeriya.”

Labarai Masu Nasaba

Sojojin Nijeriya Sun Dauki Alhakin Kai Harin Bam Cikin Kuskure A Wurin Taron Mauludi A Kaduna

SERAP  Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15

Ya ci gaba da cewa, musayar al’adu ta hanyar ilimin zamani da samar da horo a tsakanin Nijeriya da Landan, abu ne da aka shafe shekaru da dama ana yi, inda ya kara da cewa, ya samu horon zamowa jami’in soja Mons ne, a makarantar Aldershot da ke Landan daga 1962 zuwa 1963, inda ya ce, ya kuma yi kwas din jami’in zama bakaniken sufuri a makarantar soji ta koyon kanikancin sufuri ta Borden, da ke a Landan a 1964.

Buhari ya shaida wa Montgomery cewa, fahimtar banbance -banbancen al’adu da kuma girmama al’adun ne, babban ginshikin da ya sa Landan ta samu nasara, inda ya sanar da cewa, jakadun baya, sun sun kafa kyakyawar danganta da Sultan na Sokoto da kuma Sarkin Kano, Shehun Borno, da Sarkin Ilorin.

Buhari ya shaida wa Montgomery cewa, ako da yaushe, ya ci gaba da riko da ingancin jakadanci, kamar yadda jakadun baya, da aka turo Nijeriya suka yi, mussaman wajen girmama al’adun Nijeriya.

Shugaban ya bayyana cewa, Nijeriya za ta kara karfafa huldar jakadanci da ke a tsakanin Landan da kuma Sri Lanka, musamman wajen girmama al’adun kasahen biyu.

Tags: BirtaniyaBuhariGidaJakadanciSri Lanka
ShareTweetSendShare
Previous Post

Zambia Ta Shirya Jan Hankalin Sinawa Masu Zuba Jari

Next Post

Masana: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Za Ta Sa A Samu Sabuwar Damar Zamanintar Da Nahiyar Afirka

Related

Sojojin Nijeriya Sun Dauki Alhakin Kai Harin Bam Cikin Kuskure A Wurin Taron Mauludi A Kaduna
Manyan Labarai

Sojojin Nijeriya Sun Dauki Alhakin Kai Harin Bam Cikin Kuskure A Wurin Taron Mauludi A Kaduna

11 hours ago
SERAP  Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15
Manyan Labarai

SERAP  Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15

2 days ago
CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024
Manyan Labarai

CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024

3 days ago
Zaben Kano: Alkali Na Fuskantar Tuhuma Kan Kuskuren Da Aka Tafka
Manyan Labarai

Zaben Kano: Alkali Na Fuskantar Tuhuma Kan Kuskuren Da Aka Tafka

4 days ago
Shari’ar Zaben Gwamnoni: Kallo Ya Koma Kotun Koli
Manyan Labarai

Shari’ar Zaben Gwamnoni: Kallo Ya Koma Kotun Koli

4 days ago
Lallai A Rika Hukunta Masu Aikata Laifukan Zabe
Manyan Labarai

Lallai A Rika Hukunta Masu Aikata Laifukan Zabe

4 days ago
Next Post
Masana: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Za Ta Sa A Samu Sabuwar Damar Zamanintar Da Nahiyar Afirka

Masana: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Za Ta Sa A Samu Sabuwar Damar Zamanintar Da Nahiyar Afirka

LABARAI MASU NASABA

Da Na Gaba Ake Gane Zurfin Ruwa

Da Na Gaba Ake Gane Zurfin Ruwa

December 4, 2023
An Rufe Taron Fahimtar Sin Na shekarar 2023

An Rufe Taron Fahimtar Sin Na shekarar 2023

December 4, 2023
Kotu Ta Umarci Dawo Da Motoci 50 Da Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Kwashe

Kotu Ta Umarci Dawo Da Motoci 50 Da Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Kwashe

December 4, 2023
Kasafin 2024 Ya Bada Fifiko Ne Wajen Jaddada Ajandar Saisaita Nijeriya – Minista

Kasafin 2024 Ya Bada Fifiko Ne Wajen Jaddada Ajandar Saisaita Nijeriya – Minista

December 4, 2023
Gwamnatin Birtaniya Na Damuwa Kan Yadda Ake Neman A Mayar Da Kayayyakin Tarihi Da Ta Mallaka

Gwamnatin Birtaniya Na Damuwa Kan Yadda Ake Neman A Mayar Da Kayayyakin Tarihi Da Ta Mallaka

December 4, 2023
Babban Edita Dan Kasar Ghana: A Bayyana Yadda Sin Da Afirka Suke Hadin Gwiwa Da Juna

Babban Edita Dan Kasar Ghana: A Bayyana Yadda Sin Da Afirka Suke Hadin Gwiwa Da Juna

December 4, 2023
Sojojin Nijeriya Sun Dauki Alhakin Kai Harin Bam Cikin Kuskure A Wurin Taron Mauludi A Kaduna

Sojojin Nijeriya Sun Dauki Alhakin Kai Harin Bam Cikin Kuskure A Wurin Taron Mauludi A Kaduna

December 4, 2023
Jami’ar EDF: Matakan Lardin Guangdong Na Sin Kan Magance Sauyin Yanayi Abin Koyi Ne

Jami’ar EDF: Matakan Lardin Guangdong Na Sin Kan Magance Sauyin Yanayi Abin Koyi Ne

December 4, 2023
Yadda Likitocin Nijeriya 1,616 Suka Koma Aiki Zuwa Kasar Birtaniya 

Yadda Likitocin Nijeriya 1,616 Suka Koma Aiki Zuwa Kasar Birtaniya 

December 4, 2023
Xi Jinping Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Kasa Da Kasa Na Congdu Na 2023

Xi Jinping Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Kasa Da Kasa Na Congdu Na 2023

December 4, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.