Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta karrama wani dan sanda mai suna Nura Mande, wanda ya gano dala 800 kuma ya mayar wa mai kudin a Katsina.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya fitar inda ya ce dan sandan mai mukamin Constable ya samu kyautar N30,000 daga kwamishinan ‘yan sandan jihar, bisa kwatanta gaskiya da ya yi, haka kuma ya ba shi takardar karramawa.
- Idan Aka Samu Wanda Ya Fi Ni Cancantar Zama Wanda Zai Yi Wa Tinubu Mataimaki Zan Janye —Masari
- An Tisa Keyar Wani Matashi Zuwa Gidan Kaso Sakamakon Cire Mayafin Wata Mata A Kano
Nura Mande ya tsinci kudin ne dala 800 kimanin naira 480,000 kudin Nijeriya, a sansanin Alhazai na jihar a lokacin da yake aikinsa, kuma kudin na daya daga cikin maniyattan da ke sansanin ne.
Kwamishinan ‘yan sandan Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda, ya jinjina masa bisa kokarin da ya yi, inda ya ce ya nuna gaskiya da kima da kishin kasa wanda za a iya koyi da shi.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da jami’in tsaro a Nijeriya ke tsintar kudi tare da mayar da su ga mai su ba, an samu da dama kuma gwamnati ko hukumar ‘yan sanda ta karrama su tare da jinjina musu kan halin nagarta da suka nuna.