Rundunar tsaron farin kaya ta (NSCDC) a jihar Zamfara ta kama wasu mutane tara (9) da take zargi da satar Sinadarin ruwa.
Kazalika, uku daga cikin wadanda ake zargin su yi kokarin bai wa jami’an NSCDC naira dubu dari a matsayin cin hanci domin toshe bakinsu kan binciken da suke yi.
- Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 154 A Nijeriya —NCDC
- Diphtheria: Mutane 123 Sun Kamu, 38 Sun Mutu A Jihohi 4 – NCDC
Da ya ke jawabi ga manema labarai a shalkwatar rundunar da ke Gusau a ranar Alhamis, Kwamandan rundunar a jihar, Muhammad Bello Mu’azu, ya ce, mutane uku ne suka kawo cin hancin naira 100,000 a matsayin toshiyar baki domin a rufe zargin da ake musu na sama da fadi da sinadarin ruwa a jihar da suka yi.
Kwamandan ya kara da cewa, “Banki amincewa da kudin ba amma na nemi jami’anmu da su karba domin mu sami karin shaida da zamu gabatar a kotu.”
Tunin hukumar ta shigar da su kara a gaban kotu, Kara mai lambar CR/F/28/2023 a Kotun Shari’a ta 1 da ke Gusau, an kuma an dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga Mayu, 2023.
Mu’azu ya ci gaba da cewa, ‘Durom-durom na Sinadarai na ruwa da aka kama guda 70 ne, kowane durom daya a kasuwa ya kai Naira 85,000.”
Kwamandan ya ce kotun ta bayar da umarnin a ajiye motar da sauran kayayyakin a hannun hukumar har zuwa ranar 24 ga watan Mayu inda kotu za ta ci gaba da saurari karar.