Wata babban Kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano bisa jagorancin Mai Shari’a M. N Yunusa ta soke zaben sahalewar takarar zababben gwamnan Jihar Abia, Dakta Alex Otti, da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a jihohin Abia da Kano.
Kotun ta yanke hukuncin cewa nasarar da suka samu na fitowa a dama da su a babban zaben 2023 ya gudana ne ba tare da bin dokoki da ka’idojin dokar zabe ta 2022 ba.
- NNPP Ba Ta Da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu A Kotu –Buba Galadima
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bayar Da Belin Dakta Idris Abdul’aziz Bisa Sharadi Uku
Kwafin hukuncin Shari’ar da Alkalin ya yanke wanda ya fito a ranar Juma’a da safiya, kan wani Kes mai lamba FHC/KN/CS/107/2023 da Mr Ibrahim Haruna Ibrahim ke karar jam’iyyar LP da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Kotun ta ce, gazawa da rashin turawa da mika jerin sunayen mambobin jam’iyyar LP da ita jam’iyyar ta kasa yi zuwa ga hukumar INEC cikin kwanaki 30 kafin gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar ya nuna cewa hanyoyin da jam’iyyar ta bi basu inganta ba.
“Jam’iyyar ba ta bi tanade-tanaden dokar zabe ba don haka ba za a ce tana da dan takarar ba kuma ba za a ce ta ayyana wanda ya lashe zabe ba; kuri’a da aka bai wa wanda ake kara na farko, kuri’a ce kawai marar inganci,” Alkali ya zartas.