A yau ne majalisar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHA), wanda ke zama mafi girma wajen yanke shawara ta hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta yanke shawarar kin sanya shawarar shigar yankin Taiwan a taronta na shekara-shekara a matsayin ‘yar kallo a cikin ajandar taron.
A martanin da ta mayar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, wannan ya kasance ci gaba da yin watsi da shawarar dake shafar yankin Taiwan da majalisar kula da lafiya ta duniya ta ke yi na tsawon shekaru. Wannan ya nuna karara cewa, ka’idar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce fata da manufar al’ummomin duniya, kuma ba za a iya kalubalantarta ba.
A cikin wata sanarwa da hukumar WHO ta fitar ta ce, taron na WHA karo na 76, wanda aka fara jiya Lahadi, ya mayar da hankali ne kan “ceton rayuka, da samar da lafiya ga kowa da kowa.”(Ibrahim)