Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya gana da mataimakin firaministan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Christophe Lutundula jiya Litinin a birnin Beijing.
Qin ya bayyana cewa, Sin da Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo abokai ne na kwarai kana ‘yan uwan juna, wadanda ke da alakar abokantaka ta lokaci mai tsawo.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana maraba da ziyarar aiki da shugaba Felix-Antoine Tshisekedi Tshilombo zai kawo kasar Sin, kuma tana sa ran shugabannin kasashen biyu, za su fito da manyan tsare-tsare masu ma’ana, wadanda za su kai ga inganta dabarun raya dangantakar dake tsakanin Sin da DRC a mataki na gaba.
Qin ya ce, kamata ya yi bangarorin biyu su karfafa goyon baya da hadin gwiwa a MDD da sauran harkoki na kasa da kasa, da tabbatar da ka’idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da samar da daidaito a tsakanin kasashe, da tsarin tafiyar da harkokin duniya.
A nasa bangare kuwa, Lutundula ya mika godiyarsa ce ga kasar Sin, bisa muhimmin taimako da goyon baya da take baiwa kasarsa a tsawon shekaru, yana mai cewa, DRC tana tabbatar da manufar Sin daya tak a duniya.
Ya ce, DRC za ta sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, da karfafa cudanya da hadin gwiwa tare da kasar Sin, don kawo karin moriya ga kasashen da jama’ar kasashen biyu. (Mai fassarawa: Ibrahim)