Yau Talata 23 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar gudanar da dandalin tattauna ci gaban jihar Tibet ta kasar Sin na shekara ta 2023.
Cikin sakon na sa Xi ya ce, jin dadi da walwalar jama’a, hakkin dan Adam ne mafi girma, kana, samar da ci gaba na da matukar muhimmanci ga jin dadin al’umma. Don haka tun babban taron jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kawo yanzu, a karkashin goyon-bayan gwamnatin tsakiya gami da daukacin al’ummar kasar Sin, jami’ai da fararen-hula na kabilu daban-daban a jihar Tibet, suna himmatuwa matuka wajen aiki, al’amarin da ya kai ga kawar da matsanancin talauci wanda ya addabi jihar a tsawon shekaru da dama, kana an gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni a jihar tare da sauran sassan kasar. Kuma a yanzu haka ana samun ci gaba sosai a Tibet.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, a yayin da ake kokarin zamanantar da kasar Sin, ya dace Tibet ta aiwatar da sabon ra’ayin neman ci gaba ta hanyar da ta dace kuma daga dukkan fannoni, da gaggauta samun bunkasuwa mai inganci, don raya wata sabuwar jihar Tibet mai bin tsarin gurguzu irin na zamani, wadda ke da hadin-kai, da zaman wadata, da zaman jituwa, da wayewar kai, gami da kyan-muhalli, da kara samar da zaman jin dadi ga al’ummar jihar. (Murtala Zhang)