Mataimakin wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana a jiya Laraba cewa, tun daga farkon bana, Isra’ila ke ci gaba da yin gaban kanta kan batun ba da iznin komawa da gina sabbin matsugunai da halatta matsugunanta, matakin da bangaren Sin ke bukatar Isra’ilar don ta daina nan da nan, haka kuma ta daina yunkurin mamaye albarkatu da haraba mallakar Falasdinawa.
Yayin bude taro kan batun Falasdinu da Gabas ta Tsakiya da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar, Geng Shuang ya bayyana cewa, dole ne a mutunta tare da kokarin kiyaye yanayin da ake ciki a birnin Kudus.
A ranar 21 ga watan Mayu, wani babban jami’in kasar Isra’ila ya shiga Masallacin al-Aqsa, wanda ya kasance karo na biyu a bana. Lamarin da ya haddasa tsanantar yanayin da ake ciki. A cewar Geng Shuang, game da batun kare wuri mai tsarki na ibada, dole ne Isra’ila ta daina tsokana, kuma kamata ya yi ta kare hakkin Musulmai na yin sallah, da kiyaye zaman lafiya a wurin ibada, tare da mutunta ikon kasar Jordan na kula da wannan yanki.
Geng Shuang ya kara da cewa, dole ne a bi dokokin jin kai na kasa da kasa. Ya ce tun daga farkon bana, Falasdinawa fiye da 100 , ciki har da yara, sun rasa rayukansu a cikin rikici, haka kuma wasu fararen hula na Isra’ila su mu sun ji raunuka har ma wasu sun mutu.
Geng ya ce ya kamata bangarorin da abin ya shafa su daina dukkan ayyukan nuna karfin tuwo ga fararen hula, kuma su daina kai hare-hare ga makarantu da asibitoci da sauran manyan ababen more rayuwa.(Safiyah Ma)