A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi amfani da wannan lokaci, na cikar dangantakar diflomasiyyar Sin da Eritrea shekaru 30 da kafuwa, wajen karfafa daukacin fannonin hadin gwiwar sassan biyu, tare da ingiza muhimmiyar alakar kasashen biyu zuwa sabon matsayi.
Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne, cikin sakon sa na musayar taya juna murnar wannan lokaci, tare da shugaban Eritrea Isaias Afwerki, albarkacin murnar cikar dangantakar diflomasiyyar Sin da Eritrea shekaru 30.
Xi ya ce cikin shekaru 30 da suka gabata, dangantakar Sin da Eritrea ta jure sauye sauyen yanayin harkokin kasa da kasa, kuma sassan 2 sun ci gaba da kasancewa abokai na gari ga juna, sun samu ci gaba, tare da goyawa juna baya kan batutuwan da suka shafi babbar mariyar su, da wadanda suke matukar jan hankalin su.
Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada yadda yake dora muhimmancin gaske ga bunkasa alakar sassan biyu, ya kuma sha alwashin yin aiki tare da shugaba Isaias, da nufin amfani da bikin na cikar dangantakar sassan 2 shekaru 30, a matsayin wata dama ta karfafa goyon bayan juna, da yaukaka hadin gwiwa a dukkanin fannoni, da ingiza muhimmiyar dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Saminu Alhassan)