Sabon shugaban karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe da aka nada kwanan nan, Honorable Lawan Gana Karasuwa ya rasu.
A wata sanarwar manema labarai dauke da sanya hannun darakta Janar kan harkokin yada labarai na ofishin gwamnan Jihar, Mamman Mohammed ya ce, Gana ya rasu ne a asibitin Gwamnatin tarayya (FMC) Nguru bayan gajeruwar rashin lafiyar da ta riske shi.
LEADERSHIP ta labarto cewa marigayin ya taba zama Shugaban riko na karamar hukumar Karasuwa na waya shida kafin gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya sauke su.
Kazalika an sake nada shi a matsayin shugaban rikon kwanaki kalilan.
Yana daga cikin shugabannin riko 17 da gwamnan ya nada da za a rantsar da su a gobe Juma’a.
Wani abokinsa, Hon. Ado Adamu Bomboy, ya misalta marigayin a matsayin mutum mai kirki, kamala da dattako.