A baya-bayan nan, wasu cibiyoyin kasuwanci na kasashen waje a kasar Sin, sun fitar da rahotannin da ke nuna kyakkyawan fata ga kasar Sin. Misali, wani binciken da kungiyar ‘yan kasuwa ta Amurka a kasar Sin ta gudanar, ya nuna cewa, kashi 66 bisa dari na kamfanonin Amurka a kasar Sin, sun ce za su ci gaba, ko kara zuba jari a kasar Sin nan da shekaru biyu masu zuwa.
Daga watan Janairu zuwa Afrilu na wannan shekara, yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi, ya kai kusan yuan biliyan 500, wanda ya karu da kashi 2.2 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.
A cikin shekaru uku da suka gabata, yaduwar annobar COVID-19, da rikice-rikicen yanayin siyasa na duniya, sun jefa tattalin arzikin duniya cikin koma baya. Sabanin haka, kasar Sin tana da yanayin ci gaba mai dorewa, gami da samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata. Wannan babbar kasuwa dake da yawan al’umma sama da biliyan 1.4, da rukunin matsakaita masu kudin shiga sama da miliyan 400, ta jawo hankulan jarin waje kwarai da gaske.
Rahoton baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya daga hasashen karuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana, daga kashi 4.8 bisa dari zuwa kashi 5.3 bisa dari.
A halin yanzu, tattalin arzikin duniya yana fuskantar wasu kalubale a fannonin bangaranci, da ra’ayin ba da kariyar ciniki.
Wasu kasashe suna ba da shawarar “Raba gari ta fannin tattalin arziki”, gami da tsara kalmar “Magance hadari” a kokarin boye yunkurinsu na murkushe kasar Sin.
Wani rahoton bincike daga wata cibiyar bincike ta Austriya ya yi kiyasin cewa, idan Jamus ta “raba gari” da kasar Sin, GDPn Jamus zai ragu da kashi 2 bisa dari a ko wace shekara, kwatankwacin yin asarar kudin EURO biliyan 60.
John Donahoe, babban jami’in zartaswa na kamfanin Nike, ya fada a zahiri cewa “raba gari” da kasar Sin zai zama bala’i ga kasuwancin duniya. An yi imanin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zama zabin farko na zuba jari, da bunkasa kasuwanci daga ‘yan kasuwar waje.
(Mai fassara: Bilkisu Xin)