Ofishin aikin injiniya na hukumar dake lura da ayyukan sama jannati na kasar Sin, ya ce an shirya harba kumbon Shenzhou-16, da misalin karfe 9:31 na gobe Talata 30 ga watan Mayun nan.
Kumbon zai tashi ne dauke da kwamandan sa Jing Haipeng, da injiniyan sufuri Zhu Yangzhu, da kwararre a fannin dakon kaya Gui Haichao. Kaza lika yayin zaman su a samaniya, tawagar ‘yan sama jannatin za ta turke kumbon na Shenzhou-16 jikin kumbon Shenzhou-17, kafin su komawar su cibiyar saukar kumbuna ta Dongfeng a watan Nuwambar karshen shekarar nan.
A baya bayan nan, karkashin shirin binciken duniyar wata na kasar Sin mai kunshe da ‘yan sama jannati, an harba tauraron da za a yi aiki da shi. Kuma burin shi ne daga karshe a kai ga harba Basine na farko da zai sauka a duniyar wata nan zuwa shekara ta 2030, domin gudanar da binciken kimiyya, da gwaje gwajen fasahohi masu alaka da hakan.
Har ila yau, ana fatan aiwatar da manyan fasahohi masu nasaba da aikin, kamar zuwa da dawowar ‘yan sama jannati duniyar wata, da kasancewa a doron wata na dan wani lokaci, da gwada ayyukan ‘yan sama jannati da na’urori tare, ta yadda za a wanzar da tsarin binciken duniyar wata yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)