Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara kokari wajen ganin an zamanantar da karfi da tsarin tsaron kasar.
Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake jagorantar taro karo na farko, na hukumar tsaron kasa, karkashin kwamitin kolin JKS na 20.
Xi Jinping wanda shi ne shugaban hukumar, ya yi kira da kasance cikin sani da fahimtar yanayi mai sarkakkiya da kalubale da tsaron kasa ke fuskanta, da kuma tunkarar manyan batutuwan tsaro yadda ya kamata.
Ya kuma bukaci a kiyaye sabon salon ci gaban kasar ta hanyar sabon tsarin tsaro da samun sabbin ci gaba a fannin aikin tsaron kasa. (Fa’iza)