Wani jigo kuma tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Sani Al’ameen Muhammad ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya binciki kashe-kashen da aka yi a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin sanin adadin ‘yan Nijeriya da aka kashe tare da biyan diyyar rayukansu.
Al’ameen wanda ya bayar da wannan shawarar a wata tattaunawa da manema labarai a Bauchi, ya ce, zubar da jinin ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba, babban laifi ne na cin zarafin bil’adama da ya zama dole a yi bincike.
Ya ce, galibin kashe-kashen rashin hankali da garkuwa da mutane da tayar da kayar baya da sauran matsalolin rashin tsaro da ake fama da su, wasu ‘yan tsiraru ne masu son zuciya a kasar nan ne ke jagoranta, ya kara da cewa, akwai wasu jami’an tsaro da kishin gwamnatin da suke tare da ita ne kadai a tare da su.
Al’ameen wanda ya taba zama shugaban kungiyar rusasshiyar jam’iyyar AD na kasa, yayi Allah wadai da matakan da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai da tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai (rtd) suka yi, acewarsa, dukkansu sun raina matakan shari’a.