Sawun farko na maniyata aikin hajji 430 daga Jihar kebbi sun tashi zuwa kasar Saudi Arabiya don gudanar da aikin Hajjin bana.
Maniyata na Jihar ta kebbi da suka zama sawun farko zuwa kasar Saudi Arabiya sun fito ne daga kananan hukumomin Bagudo, Jega da Dandi a Jihar.
Kamfanin sufurin jirgin sama na Flynas Lion ne zai yi aikin jigilar mahajatan Jihar ta kebbi zuwa kasar Saudiya Mai dauke da Lamba A340 Airbus. A jawabinsa ga maniyatan Jihar, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bukaci maniyatan da su yi wa Jihar kebbi da kasar Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya ga dukkan jahohin kasar nan. Haka kuma ya ja kunnuwan maniyatan da su tabbatar da sun kula da kayansu da kudaden guzurinsu da aka basu daga gida Nijeriya.
Bugu da kari, Gwamna Bagudu yayi musu fatar Alhairi da kuma gudanar da aikin Hajji karbabiya.
Shima a nashi jawabi, Amirul-Hajj na Jihar, Minista Abubakar Malami ya bayyana wa maniyatan cewa” Gwamnatin Jihar kebbi tayi tanadi ga kwamiti don kula da maniyata tun daga nan gida har kasar Saudi Arabiya. Haka kuma an hada mambobin kwamiti kwararu don tabbatar da cewa an gudanar da aikin Hajj kyaukyawa, inji Minista Abubakar Malami a matsayin Amirul-Hajj yayin jawabi ga maniyatan”.
Haka zalika ya bukaci su da subi doka da oda na kasar Saudiya yayin gudanar da aikin Hajji a kasar. Ya kuma yi musu fatar Alhairi da kuma rokonsu na su yi wa kasar da Jihar kebbi addu’ar samun zaman lafiya da magance matsalar tsaro, inji Amirul-Hajj”.
Daga karshe Wakilinmu ya ruwaito cewa” kimanin maniyata fiye da dubu biyu ne ake saran zasu gudanar da aikin Hajjin bana daga Jihar kebbi”.