• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Matashi Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 10 Fyade A Bauchi

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Fyade

Wani matashi mai shekara 33 a duniya, ana zarginsa da yin amfani da sinadarin da ke sanya maye wajen gusar da hankalin wata karamar yarinya ‘yar shekara 10, tare da yi mata fyade a karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi.

Matashin wanda ya yaudari yarinyar ta hanyar ba ta lemo da ake zargin na dauke da sinadarin da ke sanya maye domin samun damar lalata da ita ba tare da saninta ba.

  • Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa
  • Tinubu Ya Shiga Wata Ganawa Da Gwamnonin Jam’iyyar APC A Abuja

A cewar wata sanarwar manema labarai da kakakin ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, wanda ake zargin ya samu damar fyade da yarinyar ne ta hanyar amfani da karfin tsiya.

Ya ce, “A ranar 25 ga watan Mayun 2023, wani mutum da ke kauyen Nasaru a karamar hukumar Ningi ya kai rahoto caji ofis din ‘yansandan Ningi, inda ya ce wani matashi da suke gari daya ya yaudari ‘yarsa mai shekara 10 ta hanyar ba ta lemo da ake zargin na dauke da sinadarin da ke sanya maye wanda hakan ya sanya hankalinta ya gushe.

“Ya yi amfani da wannan damar ya yi mata fyade, wanda ya hakan ya sanya yariyar ta gamu da raunuka a al’aurarta kana ta yi ta zubar da jini.”

LABARAI MASU NASABA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

A fadin sanarwar, tun lokacin da suka amshi rahoton, tawagarsu cikin hanzari suka garzaya inda lamarin ya faru tare da daukar yarinyar zuwa babban asibitin Ningi daga bisani aka sauya mata wurin jinya zuwa asibitin kula da masu yoyon fitsari (NOFIC) da ke Ningi, bayan kaurin jikinta aka sake nausawa da ita zuwa asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa domin neman kulawar likitoci.

A cewar Wakil, tun lokacin ‘yansanda suka sha alwashin sai sun cafko wanda ya aikata hakan domin tabbatar da yarinyar ta samua adalcin da ya dace ta samu, “Kan hakan mun cafke wanda ake zargi, Danladi Ibrahim.

“A lokacin da ake tuhumarsa, ya amsa da kansa cewa ya aikata laifin, don haka bincike na cigaba da guduna da zarar aka kammala za mu gurfanar da shi a gaban kuliya.”

Daga bisani rundunar ‘yansandan ta jawo hankalin al’umma da cewa suke sanya ido da lura da yankunansu domin dakile aniyar bata gari a kowani lokaci tare da gaggawar kai rahoton faruwar lamuran da ba daidai ba cikin hanzari domin daukan matakan gaggawa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)
Manyan Labarai

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri
Labarai

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Next Post
Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.