Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) za ta fara yajin aikin gama gari daga ranar Laraba mai zuwa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin mai a fadin kasar sakamakon jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na cire tallafin man fetur.
- Yadda Matashi Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 10 Fyade A Bauchi
- Tinubu Ya Nada Akume Da Femi A Sakataren Gwamnati Da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero a ranar Juma’a ne ya bayyana hakan bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na kungiyar a Abuja.
Ya ce gwamnati, dole ta mayar da farashin man fetur da ake sayarwa a baya.
Ajaero ya kara da cewa rashin cika wa’adin da gwamnatin tarayya ta yi zai janyo zanga-zangar da ba za a taba mantawa da ita ba a fadin kasar nan.