• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Dakatar Da “Wasan Matsorata” Da Jam’iyyun Siyasan Amurka Suke Yi Amma Damuwa Ta Dore

by CMG Hausa
2 years ago
Amurka

Bayan da majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da kudurin doka game da aikin kayyade basussuka da kasar za ta iya karba, kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun bayyana a jiya Alhamis cewa, batun nan tamkar “dakatar da yaki na wucin gadi ne, wanda ba a kawo karshensa ba tukuna”.

Kudurin ya dakatar da lokacin fara yin amfani na dokar kayyade yawan bashin da gwamnatin kasar Amurka za ta iya ci har zuwa farkon shekarar 2025, haka kuma an kayyade kudaden da za a kashe a cikin kasafin kudi na shekarar 2024 da ta 2025.

  • Jami’an Kasuwancin Sin Da Amurka Sun Amince Da Karfafa Muamala

Ga alama batun nan ya kau da damuwar wasu mutane. Sai dai ko da majalisar dattawa ta kasar Amurka ta amince da kudurin a nan gaba, kuma shugaban kasar shi ma ya sanya masa hannu, shin da gaske ne za a iya warware matsalar ta wannan dabara? Shin da gaske ne Amurka din da sauran sassan duniya suna cikin wani yanayi mai tsaro yanzu?

A halin yanzu, a kasuwannin takardun bashi na kasa da kasa an fi samun takardun shaidar bashin da ake bin gwamnatin kasar Amurka. Saboda haka idan gwamantin kasar Amurka ta kasa biyan bashin, to, ita kasar da sauran kasashe daban daban za su shiga cikin mawuyacin hali. Don tinkarar wannan yanayin da za a iya samu, kasar Amurka ta dauki wannan dabara: wato a dakatar da lokacin fara aiki na dokar kayyade bashin da za ta iya karba da tsawon shekaru biyu. Ko da yake wannan dabara ta dakatar da matsala kawai, maimakon warware ta daga tushe. Ban da haka kuma za ta sanya bashin da kasar Amurka ta ci dinga karuwa.

A matsayinta na kasa mafi tasirin tattalin arziki a duniya, muhimman alkaluman ma’aunin tattalin arzikin kasar Amurka na ci gaba da raguwa, kana ana fuskantar babban hadarin samun koma bayan tattalin arzikin kasar, yayin da dimbin bankunan kasar ke fuskantar mawuyacin hali, lamarin da ya haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga sauran sassan duniya.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Yanzu, rikicin bashi na Amurka, wanda aka kwashe watanni da dama ana tinkararsa, yana ci gaba da haifar da matsaloli a kasuwannin kasa da kasa. Daga cikin wannan “wasan matsorata” da jam’iyyun siyasan kasar Amurka suke yi, wanda ba a san lokacin da za a kawo karshensa daga tushe ba, wani ilimin da mutanen duniya suka samu shi ne, kasar Amurka ce ke haifar da babban hadari ga tattalin arzikin duniya.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani
Daga Birnin Sin

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 
Daga Birnin Sin

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

October 14, 2025
Next Post
Yadda Aka Kammala Gasar Firimiya Ta Bana

Yadda Aka Kammala Gasar Firimiya Ta Bana

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.