Kadarorin tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ba su karu ba a tsawon shekaru takwas da ya kwashe yana mulki, cewar kakakin, Malam Garba Shehu.
Shehu ya ce ana iya ganin hakan a cikin fom din bayyana kadarorin da ya mika wa Hukumar da ke da alhakin kididdige kadarori.
- Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari
- Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari
A cewar Shehu, bayanan da suka bayyana sun nuna cewa kadarorin da Buhari ke da su ba su karu ba, a gida Nijeriya ko a waje kuma bai kara sabbin asusu na banki ba fiye da daya tilo da yake da shi a bankin Union, Kaduna.
“Bai karbi lamuni ba kuma bashi da wani alhaki nauyin wani a kansa. Adadin dabbobin da ke gonarsa ya ragu kadan saboda ya bayar da su kyauta a cikin shekaru hudun da suka gabata,” in ji Shehu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.
Fom din na bayyana kadarorin ya zama tilas ga duk zaɓaɓɓun jami’an gwamnati su bayyana kadarorin su da kuma kudaden da ake bin su a kan karagar mulki da kuma a karshen wa’adinsu.