Biyo bayan turo Tumatir da kasashen Ghana da Kamaru suka yi zuwa wsu manyan kasuwannin Nijeriya, hakan ya janyo farashin na Tumatir ya karye.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, a kwanukan baya a Nijeriya biyo bayan bullar cutar da ke harbin Tumatir da aka shuka a gonakai wadda ake kira a turance, Tuta Absoluta ta haifar da karancin Tumatir a wasu sassan kasar nan tare da kuma hauhawan farashin na Tumatir a kasar.
Wannan ne ya sa manyan masu hada-hadar kasuwancin na Tumatir da ke a kasar nan a suka yanke shawarar shigo da Tumatir daga kasashen na Ghana da kuma Kamaru.
Har ila yau, binciken da aka gudanar ya nuna cewa, farashin Kwandon Tumatir daya, a jihar Kano wanda a baya ake sayarwa Naira 50,000 a wasu sassan kasar nan, a yanzu, ana sayar da Kwandon daya kan Naira 18,000 zuwa Naira 20,000,musamman saboda an samar da wadataccen sa.
A cewar shugaban kungiyar manoman Tumatir na kasa reshen jihar Kano (TOGAN), Alhaji Sani Danladi Yadakwari, karancin na Tumatir da aka fuskanta a baya, ya faru ne saboda harbin da cutar ta Tuta Absoluta ta yiwa Tumatir da aka shuka a gonakai da ke a cikin jihar ta Kano.
Yadakwari ya bayar da tabbacin cewa, amma biyo bayan turo Tumatir da aka yi daga jihar Ogun da kuma sauran wasu kasashen da ke a nahiyar Afirka kamar su, Ghana da Kamaru, hakan ya janyo farashin na Tumatir ya karye.
“A yanzu dai, karancin na Tumatir da aka fuskanta a baya, ya faru ne saboda harbin da cutar ta Tuta Absoluta ta yiwa Tumatir da aka shuka a gonakai. ”
A cewarsa, “Amma biyo bayan turo Tumatir da aka yi daga jihar Ogun da kuma sauran wasu kasashen da ke a nahiyar Afirka kamar su, Ghana da Kamaru, hakan ya janyo farashin na Tumatir ya karye.”
Shugaban ya bayyana cewa, biyo bayan shigo da Tumatir da manyan masu hada-hadar kasuwancin sa a kasar nan daga kasashen Ghana da kuma Kamaru, bakan ya sa an samu nasarar karya farashin na Tumatir a kasuwannin kasar nan.
In ba a manta ba, a makwannin baya ta na sayen Kwandon Tumatir a wasu sannan kasar nan ya kai Naira 17,000 zuwa Naira 18,000, inda farashin ya tashi zuwa Naira 48,000.
Har ila yau, a garin Fatakwal an sayar da Kwadon Tumari kan Naira 65,000 zuwa Naira70,000, inda a Enugu, ake sayar da Kwandonsa daga Naira 63,000 zuwa Naira 68,000, wannan ya danganta da irin kasuwar.