Wani hatsarin mota da ya afku a garin Zakirai da ke kan hanyar Kano zuwa Ringim a karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano, ya ci rayukan fasinjoji 18.
Lamarin da ya faru a sakamakon makare wata mota da lodin kaya, ya hada da wasu motocin kasuwanci guda biyu, inda ya yi taho mu gama da wata motar bas.
- Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano – FRSC
- Mutum 3 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar hatsarin.
Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a.
“Mun samu waya game da hadarin da misalin karfe 8:35 na dare a ranar Juma’a kuma muka tura jami’an mu wurin domin ceto wadanda abin ya shafa,” inji shi.
“Hatsarin ya rutsa da fasinjoji 35 a cikin motocin bas guda biyu, daga ciki 18 sun kone kurmus, yayin da wasu 12 suka samu munanan raunuka.”
Da yake jajantawa, Abdullahi ya koka game da yawaitar samun hadurran a jihar Kano cikin makon da ya gabata.
A ziyarar da ya kai wurin da hatsarin ya afku a ranar Asabar, ya gargadi masu ababen hawa, musamman masu zirga-zirgar ababen hawa da na jahohi, da su guji wuce gona da iri yayin tuki.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin samun kulawar gaggawa.
A halin da ake ciki, an yi jana’izar wasu da suka mutu a wurin da hatsarin ya afku, yayin da wasu kuma aka mika su ga ‘yan uwansu.
Bisa la’akari da yawaitar hadurran kan tituna a baya-bayan nan, hukumar FRSC ta yi alkawarin kara wayar da kan jama’a tare da tabbatar da tsauraran matakan tsaro.
Waɗannan yunƙurin sun haɗa da aikin kotunan tafi-da-gidanka don ladabtar da masu karya ka’idojin tuki cikin gaggawa da tabbatar da bin ka’idojin kiyaye hanya.
An yi kira ga masu ababen hawa da su ba da fifiko ga tsaro, da kuma guje wa wuce gona da iri yayin tuki da duk wani yunkuri da ka iya kawo hatsari ga kansu da sauran mutane a kan hanya.
Al’umar yankin da mahukunta sun yi matukar alhinin asarar rayukan da aka samu a wannan mummunan hatsarin, kuma sun ci alwashin tsayawa tsayin daka a kokarinsu na hana afkuwar hadura a kan tituna.