A ranar 20 ga watan nan ne aka rufe taron tattaunawa na Shangri-La karo na 10 a kasar Singapore.
A gun taron na wannan karo, jagororin sassan tsaro, ko shugabannin tawagogi na kasashen Sin, da Mongoliya, da New Zealand, da Philippines, da Cambodia, da Malaysia, da Jamus, da Birtaniya, da Australia, da Japan, da Koriya ta kudu, da Indonesia, da kungiyar tarayyar Turai, sun yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakaninsu, da yanayin da ake ciki a duniya, da shiyya shiyya, da ma sauran batutuwan da ke daukar hankulansu duka.
Bayan taron, tawagar masana mahalarta taron sun bayyana wa manema labarai cewa, kasar Sin na daukar hakikanin matakai wajen kiyaye tsaron duniya, don haka ma ta samu amincewa daga gamayyar kasa da kasa.
Masanan sun kara da cewa, taron Shangri-La dandali ne na tattauna harkokin tsaro a maimakon rura wutar nuna fin karfi. Tawagar kasar Sin ta halarci taron ne domin tabbatar da zaman lafiya da hadin gwiwa da ma ci gaba. (Lubabatu)