Litinin din nan ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya jagoranci taron manema labarai da aka saba gudanarwa.
Wani dan jarida ya yi masa tambaya cewa, “Mun lura cewa, a yayin tattaunawar Shangri-La da aka gudanar a ‘yan kwanaki da suka gabata, jami’an kasashen Indonesia, da Singapore da sauran manyan jami’ai sun bayyana cewa, ba su son ganin ‘sabon yakin cacar baka’, kuma ba su so a tilasta musu zabar wani bangare tsakanin Sin da Amurka, mene ne ra’ayin kakakin kan wannan batu?”
Wang Wenbin ya ce, cikakkun bayanai sun nuna cewa, kasashe daban-daban na da niyyar kaddamar da “sabon yakin cacar baka” a yankin Asiya, lamarin da ya tilasta wa kasashen yankin zabin bangarori, lamarin da ya haifar da taka-tsan-tsan da nuna adawa mai tsanani daga kasashen yankin. Burin bai daya na kasashen yankin, shi ne riko da ‘yancin cin gashin kai bisa dabaru da kuma kiyaye zaman lafiya da ci gaban yankin.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, wasu kasashe na da’awar cewa, suna da ‘yanci da yin komai a bayyane, suna ikirarin tabbatar da zaman lafiya da wadata a yankin, amma a hakikanin gaskiya, a kullum suna hada kan kungiyoyin soji daban-daban, suna kokarin tura kungiyar tsaro ta NATO daga gabashi shiga yankin Asiya da tekun Pasifik.
Dangane da haka, halin da galibin kasashen yankin ke ciki a fili yake: suna adawa da matakin da kungiyoyin soja daban-daban suke yi a yankin, ba su maraba da NATO ta fadada ikonta a nahiyar Asiya, sannan kuma ba su fatan ganin sake barkewar wani sabon yakin cacar baka a yankin Asiya. (Mai fassarawa: Ibrahim)