Jami’ar Lincoln da ke Birtaniya ta dakatar da Tsohon Kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu daga yin duk wata hulda da shi ciki har da kasancewarsa Farfesa mai kai ziyara a Jami’ar.
Jami’ar, ta dauki matakin ne biyo bayan zargin Ekweremadu da yin safarar dan shekara 16 zuwa kasar don a cire wani sashe daga jikinsa.
- 2023: Kwankwaso Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Watsi Da APC Da PDP
- Hajjin Bana: Sawun Farko Na Maniyata Aikin Hajji 430 Sun Ta Shi Daga Kebbi
A yanzu haka dai, Ekweremadu da mai dakinsa Beatrice, na garkame a gidan yarin Birtaniya kan tuhumar zargin da wata kotun kasar ke tuhumarsu.
Amma Ekweremadu da Beatrice, sun karyata zargin nasu da ake yi kan lamarin.
An ruwaito mai magana da yawun Jami’ar ya ce, Mahukunta Jami’ar sun kadu matuka kan irin yanayin zargin da ake wa Ekweremadu, inda suka kara da cewa binciken ‘yan sanda ne zai tabbatar da gaskiyar lamarin kuma ba za su iya yin wani dogon bayani, kan lamarin a wannan matakin ba.