Wanda ake tuhumar na fuskantar tuhume-tuhume uku da suka hada da hadin baki da shi, domin yaudara wurin cin kudin, wanda sashen yaki da masu damfarar na ‘yansanda na musamman yake tuhumarsa da shi.
An gurfanar da Nwogu ne tare da kamfaninsa, Libelihood Homes Limited, da sauran wadanda ake tsare da su a gaban mai shari’a Peter Lifu.
- Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Da Japan Ke Shirin Yi Zai Illata Duk Fadin Duniya
- Kotu Ta Bukaci Masu Kalubalantar Nasarar Tinubu Su Biya Miliyan 10 Kowannensu
Dansanda mai shigar da kara, Emmanuel Jackson, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma da sauran abokansa yanzu, sun aikata laifin ne a cikin wannan shekarar.
Jackson ya shaida wa kotun cewa sun damfari cocin naira miliyan 65 daga wani coci da ke unguwar Ojodu a Jihar Legas ta hanyar yi mata karyar kamfaninsa na da filayen sayarwa a Karamar Hukumar Ewekoro Jihar Ogun da Agbara babban titin a Legas tare da yin karyar cewa suna da filayen sayarwa a Karamar Hukumar Ewekoro. Jihar Ogun, da Agbara, Badagry Edpressway a Legas, ya ce shi da jama’arsa ne suka karbi kudin.
Ya ce bayan karbar kudin daga cocin, wanda ake kara ya kasa bayar da filin kamar yadda ya yi alkawari, sannan kuma ya kasa biyan cocin kudin.
A cewarsa, laifukan sun ci karo da sashe na 8 (a), 1 (1) (8) da kuma hukunci a karkashin sashe na 1 (3) na kudin zamba da sauran laifuka masu alaka da zamba, mai lamba 14 na 2006 da sashe na 15(2) (b) na Dokar Hana Cin Kudin Zamba na shekarar 2011 kamar yadda aka gyara a 2012.
Amma kuma abin mamaki Nwogu ya musanta zargin da ake masa.
Bayan da ya shigar da kara, dansandan ya bukaci kotun da ta ci gaba da sauraren karar, sannan kuma ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan yari na Nijeriya har sai an kammala tantance zargin da ake yi masa.
Sai dai lauyan wanda ake tuhuma, Bernard Omang, ya nemi kotun da ta amince da wanda yake karewa da bayar da belinsa cikin sharudan sassauci.
Kotu ta yi watsi da bukatar tasa bisa hujjar cewa babu wata bukata da ta dace da za ta goyi bayan bukatarsa.
Don haka mai shari’a Lifu ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma a gidan yari na Ikoyi sannan ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 14 ga watan Yuni.