Rundunar Sojin Nijeriya ta 14, Ohafia, ta kai samame a wata masana’antar jarirai da ke Umunkpei Nbosi a Karamar Hukumar Isiala-Ngwa a Jihar Abia, wanda ake zargin wani Dan yankin ne ke sarrafa ta.
Dakarun sun isa wurin ne inda suka ceto mata 22 daga cikinsu 21 na dauke da juna biyu ciki har da jarirai 2 (maza da mace data).
- Gwamnatin Abba Kabir Za Ta Inganta Tsarin Makarantun Tsangayu A Kano – Falaki
- Yanzu-Yanzu Tinubu Na Ganawa Da Kwakwaso
Sauran kayayyakin da aka samu a wurin sun hada da janareta Tiger, wayoyin wuta, tukunyar gas, buhun shinkafa, tumatur kwali guda, man kayana marmari 4, buhunan garri 5, da kuma kayan miya leda 2.
Sojoji sun kai samame a masana’antar jarirai ne biyo bayan rahoton sirri da aka samu cewa mai kamfanin na sayar da wasu jariran ga ‘yan fashi da makami domin yin tsafi da su, wasu kuma domin safarar yara.
An yi zargin cewa wata ma mata tana da take zaune a yankin tana mu’amala da su kuma a wasu lokutan, ana ganin sassan jikin mutane a kusa da ginin gidanta.
A cewar wani mamban rundunar, mai kamfanin jariran a halin yanzu yana nan a hannun rundunar ana ci gaba da kamo sauran domin gudanar da bincike.
Sai dai rundunar sojin ta kama wata mata mai suna Katherine Oyechi Ngwanma, mai shekaru 34, mai dafa abinci a wurin.
Matan masu juna biyu, da jariran, an mika su ga gwamnatin Jihar Abia domin ci gaba da kula da su.
Ba a iya samun sabon jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda a jihar, Chinaka Maureen, domin jin ta bakinsa ba.
Sojojin sun samu jagorancin jami’in hulda da jama’a na rundunar soji, Brigade Ohafia 14, Laftanar Omale Innocent Prince, da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai Aled Otti, Mista Ferdinand Ekeoma.
A wata hira da aka yi da shi bayan aikin, Ekeoma ya yaba wa rundunar sojin bisa aikin, inda ya bayyana cewa babu hujjar dalilin da ya sa “irin wannan abu ya kamata ya faru a kowane yanki na Jihar Abia”.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Aled Otti za ta tsaftace jihar, yayin da gwamnati tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Gwamnatin Otti, in ji shi, ba za ta bari irin wannan lamari ya ci gaba ba a kowane bangare na jihar ba daga yanzu.