ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

by Rabi'u Ali Indabawa
10 months ago
Bauchi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama akalla mutum 11 da ake zargi da hannu a kisan wani matashi mai shekaru 29, mai suna Ahmad Lawan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Ahmed Wakil, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa, yana mai cewa ana ci gaba da neman sauran wadanda suka tsere.

  • Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
  • Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

A cewar Wakil, wadanda aka kama sun hada da: Abdulwahab Adamu, mai shekara 25; Nuruddeen Idris, mai shekara 21; da Kabiru Saidu, mai shekara 25; sai Ibrahim Hamza, mai shekara 22; da kuma Abdullahi Isah, mai shekara 21.

ADVERTISEMENT

Sauran su ne: Abdulrasheed Garba, mai shekara 25; Abdulwahab Abubakar, mai shekara 25; Kabiru Muhammad, 27; Musa Abdullahi, 24; Umar Muhammad, 25; da Umar Ali, 27.

Yayin bayyana cikakken rahoton lamarin, mai magana da yawun ‘yansandan ya ce marigayin an daba masa wuka a kirji ta hannun mutum biyu da suka tsere bayan harin.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Sanarwar ta ce, “A ranar 2 ga Oktoba, 2025, misalin karfe 08:25 na safe, wani mutumin kirki ya kai rahoton kisan gilla a ofishin D Dibisional Police Headkuarters.

“Rahoton ya bayyana cewa wasu mutane biyu sun je gidan wani Ahmad Lawan, namiji, mai shekaru 29, wanda ake kira Soje, mazaunin Sabon Kasuwa, wanda ake zarginsa a matsayin shahararren dan sara-suka.”

“Suka kwankwasa kofar gidansa, bayan da ya bude, sai suka soka masa wuka a kirji sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.”

Wakili ya bayyana cewa jami’an da ke karkashin D’ Dibision, karkashin jagorancin DPO CSP Mubarak Sani Baba, “sun hanzarta zuwa wurin da abin ya faru, suka dauki wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.”

Ya kara da cewa an mika gawar ga iyalansa domin a yi masa jana’iza bisa tsarin Musulunci.

A cewar binciken farko, ‘yansanda sun gano Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Duduwa, da Abubakar Mohammed, a matsayin manyan masu hannu a kisan.

Bayan an binne Lawan, Wakil ya ce wasu fusatattun matasa sun kai farmakin ramuwar gayya inda suka kona gidan iyalin daya daga cikin wadanda ake zargi.

“Amma hadakar jami’an Rapid Response Skuad, Operation Restore Peace da D’ Dibision suka iso da gaggawa suka dakile rikicin,” in ji shi.

‘Yansanda sun kara bayyana cewa daya daga cikin manyan wadanda ake zargi, Abubakar Ibrahim (Duduwa), wanda ya fara tserewa, daga baya an gan shi yana yawo a Mararraban Liman-Katagum, kuma jami’an tsaro na sa-kai suka kama shi.

“Yayin da ake kai shi ofishin ‘yansanda, wasu fusatattun matasa suka tare su a Kwanar Kwaila suka kai masa hari da takubba, wanda ya jawo karaya a hannuwansa biyu da kuma mummunan rauni a kansa,” in ji Wakil.

Ya ce jami’an ‘yansanda sun iso da gaggawa inda suka ceci wanda ake zargin, suka tarwatsa matasan, sannan suka garzaya da shi ATBUTH domin jinya.

Sanarwar ta kara da cewa duk wadanda aka kama suna kan bincike domin tantance irin rawar da kowane dayansu ya taka a lamarin.

Wakil ya ruwaito Kwamishinan ‘Yansanda, CP Sani-Omolori Aliyu, yana gargadin iyaye da shugabannin al’umma da su ja kunnen ‘ya’yansu kada su bari a yi amfani da su wajen tayar da hankalin jama’a.

“Rundunar ba za ta yi wata-wata ba wajen daukar mataki mai tsauri kan duk wanda ko wata kungiya da gangan ta kawo tabarbarewar doka da oda ta kowace siga. Duk wanda aka kama da laifi za a hukunta shi bisa cikakkiyar doka,” in ji Aliyu.

Ya kara da cewa an tura tawagogin jami’an musamman a sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da bin doka da oda yadda ya kamata.

A tuna cewa, kamar yadda jaridar PUNCH Metro ta ruwaito a 2024, rundunar ta taba kama wasu mutane makamantan wadannan bayan kisan gilla da aka yi wa wani Adamu Alkasim a unguwar Bayan Gari, Bauchi.

A lokacin, an kama mutum biyu Usman Shehu, mai shekara 20, da Abdullahi Abubakar, mai shekara 19, bisa zargin “hada baki wajen aikata laifi da kuma kisan kai.”

Bauchi
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.