Kasar Sin ta zargi Amurka da cin zarafi ta hanyar yunkurin kwace mata matsayin kasancewa kasa mai tasowa, tana mai cewa matakin ba Washington ce ta yanke hukunci a kai ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton cewa, a jiya Alhamis ne kwamitin majalisar dattijan Amurka mai kula da harkokin wajen kasar, ya zartas da wani kudiri da ake kira wai “Dokar kawo karshen matsayin kasar Sin na kasancewa kasa mai tasowa,” daftarin dokar da zai bukaci ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkar, ta yi kokarin sauya matsayin kasar Sin a matsayin kasa mai tasowa a cikin kungiyoyin kasa da kasa.
Da aka tambaye shi don yin karin haske game da wannan batu yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan a birnin Beijing, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce wannan mataki da Amurka ta dauka, kawai wani salo ne na neman dakile ci gaban kasar Sin.
Ya ce, ko kasar Sin kasa ce mai tasowa ko a’a, wannan bai shafi Amurka ba. (Mai fassarawa: Ibrahim)