Masu karatu assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a wannan makon a filin naku mai matukar farin jini na Ado Da Kwalliya.
‘Yan uwana mata yau filin naku zai tabo wani batu ne mai muhimmanci kan abin da ya shafi adon da muke yi a kusan kullum. Batun kuwa shi ne daurin dankwali. Da yawa na san za su yi mamaki su ce daurin dankwali kuma? Eh, haka ne, daurin dankwali abu ne da za a iya cewa ya zama cikar kwalliya a wurin ‘ya mace musamman Bahaushiya, domin al’adarmu da addininmu duka sun yi mana nuni da shi.
To sai dai a wannan zamanin, ana samun wasu yara mata da kan kasa daura dankwalinsu kamar yadda ya kamata.
Misali, wata idan ta daura, kai ka ce dankwalin zai bi hanyar katon dutsen nan na Abuja ne da ake ce wa Zuma Rock, ma’ana daurin bai yi ba, a rasa gane ma’anarsa, ita bai mata kyau ba kuma bai rufe mata gashin kanta ba. Don haka yau nake son nusar da ‘yan’uwana mata masu irin wannan daurin a kan abin da ya dace su yi.
Da farko dai kafin mace ta yi daurin dankwali, ya kamata ta muhimmanta rufe gashin kanta, domin duk adon da za ta yi ya ja mata tsinuwa a wurin Mahalicci bai cancanta da ita ba.
Kodayake akwai wacce za ta iya yi saboda mijinta na halas malak shi kadai, to irin wannan ya halatta.
Shi daurin dankwali kala-kala ne, akwai wanda ake yi da gyale, akwai kuma wanda ake yi da dankwali na kayan da aka dinka ko dankwali na abaya.
Galibin dankwalin da ake daurawa mai yawan zagaye da gyale ake yin sa. Misalin mai sauki a ciki, idan kika ninke gyale, sai ki yafa a kanki, ki kama tsawonsa na bari da bari, ki dawo da shi gaba, sai ki kama na bangaren hagu ki dawo da shi dama, na bangaren dama ki dawo da shi hagu, sai ki kulla a gaban kanki sau biyu.
Daga nan sai ki koma da su baya duka biyun ki kulla daidai kasan keyya.
Irin wannan dankwalin ko harami za ki je da shi saboda ya rufe kanki luf-luf kuma yana kawata mace.
Misali na biyu kuwa shi ne idan za ki yi da atamfa, misali kalar wadda za ki yi wa maigida wanda idan ya dawo zai ji kamar ya kama kujera ya dake yana kallonki kawai, idan kika dauko dankwalin sai ki rubanya shi biyu, daga nan ki kama gabansa (wurin da ya fi tsawo) shi ma ki rubanya sau biyu (idan kuma akwai head ban) sai ki saka a cikin dankwalin, daga nan ki sake rubanyawa sau daya.