Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya roki zababbun Sanatoci da su zabi tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, a matsayin shugaban majalisar Dattawa ta 10 da za a kaddamar a gobe Talata.
Shettima ya bayyana haka a ranar Asabar a wajen liyafar da aka shirya domin neman goyon baya tikitin takarar, Akpabio da Jibrin Barau, ya ce, a shirye yake ya sanya guiwowinsa kasa ga Sanatoci don su amince da wannan tikitin.
- Ba Ma Kokarin Musuluntar Da Nijeriya –Shettima
- Dole Mu Yi Gaggawar Cire Tallafin Mai Ko Ya Halaka ‘Yan Nijeriya – Shettima
Ya ce, zaman Akpabio shugaban Majalisa Dattawan, manufa ce mai kyau na tabbatar da zaman lafiya da hadin kan Nijeriya.
“A shirye nake na durkusa na roki abokaina don su biyo wannan ayarin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa.” Cewar Shettima.
Liyafar ta hada fuskokin Sanatoci sama da 50 da Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume.
Shettima ya ce, “Baya ga bangaren addini ma, Sanata Akpabio ya cancanta yana da cikakken rinjaye da zai iya jagorantar Majalisar kasa ta 10. A gefe guda, ya kuma fito daga shiyya mai matukar muhimmanci sannan shi din kirista ne mai biyayya.
“Don haka bisa kundin tsarin mulkin kasa da manufofin jam’iyyarmu da bukatar wanzar da hadin kanmu, ya dace a mara masa baya.”
Mataimakan Shugaban kasan ya kuma bai wa zababbun Sanatocin tabbacin goyon bayansa wajen ganin an samu nasarar kai Akpabio matsayin shugaban majalisar ta hanyar bibiya da tuntubar sauran Sanatocin da ba su halarci liyafar ba.