Kasar Amurka ta fara shirye-shiryen tallafawa kasar Ukraine da makami mai linzami don yakar Rasha a yakin da suke tafkawa da juna.
Shugaban Amurka, Joe Biden ne ya bayyana haka, inda ya ce yanzu shi ne lokacin da fi dacewa a kai wa Ukraine dauki daga cin zarafin da Rasha ke mata.
- Zargin Cin Hanci: Alkalin Alkalai, Tanko Muhammad Ya Ajiye Mukaminsa
- An Tsinci Wani Yaro An Kwakwule Masa Idanu A Bauchi
Rahotanni sun bayyana cewar ana sa rai, a cikin wannan satin Amurka za ta fara aike wa Ukraine da makaman wanda suka hada da makaman kare dangi.
Kasashen Yammacin Turai da Majalisar Dinkin Duniya, sun sha sukar Rasha kan irin mamayar da ta yi wa Ukraine.
Yakin ya salwantar da rayukan dubban mutane a Ukraine.
Har ila yau, Rasha ta kwace iko da wasu birane da ke makwabtaka da kasarta, inda suka dawo karkashin ikonta.