A farkon wannan wata jaridar Washington Post ta rawaito cewa, yawancin manyan kasashe masu karfin faɗa a ji a cikin kasashe masu tasowa na ci gaba da nuna ƙyama ga kasashen yamma da Amurka, kuma wadannan dabi’un sun samo asali ne daga yanayin “wuyarmu ta yi ƙauri”.
Rahoton ya ce, a cikin shekaru ashirin da suka wuce, an samu gagarumin sauyi a tsarin kasa da kasa. Kasashen da a da suke da yawan jama’a amma matalauta sun tashi daga kan iyaka zuwa mataki na tsakiya.
Kuma a da suna wakiltar kaso da bai taka kara ya karya ba a tattalin arzikin duniya, yanzu kasashe masu tasowa su ne kaso rabi na kasuwar duniya. Ba laifi ba ne idan an ce sun kawo karfi.
Yayin da wadannan kasashe suka samu karfin tattalin arziki, da kwanciyar hankali a siyasance da kuma alfahari da al’adunsu, su ma sun zama masu kishin kasa, kuma ana bayyana kishin kasarsu a matsayin adawa da kasashen da suka mamaye tsarin kasa da kasa wato kasashen yamma. (Mai fassarawa: Yahaya)