Ranar 15 ga watan Yunin bana ne aka cika shekaru 22 da kafa Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai ko kuma SCO a takaice.
A cikin shekaru 22 da suka gabata, kungiyar ta kasa da kasa da aka sanya wa sunan wannan birni na kasar Sin wato Shanghai ta samu ci gaba, kuma ta zama wani jigo mai amfani a cikin yankin Turai da Asia da harkokin kasa da kasa.
A matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar, kasar Sin a ko da yaushe ta himmatu wajen inganta ci gaban kungiyar ta SCO.
Tun daga shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci dukkan tarukan koli na kungiyar SCO, inda kuma ya gabatar da wasu shawarwari masu muhimmanci, wadanda suka ba da jagora da kuzari kan ci gaban kungiyar, da kuma yin hadin gwiwa a yankin, tare da jagorantar ci gaban kungiyar cikin dogon lokaci ba tare da wata matsala ba ta hanyar yin amfani da “hikimar kasar Sin”.
A nan gaba, yayin da kungiyar ta SCO ke shiga shekaru goma na uku, yana da kyau a lura da yadda za ta fara sabuwar tafiya da kuma wace irin karfi ce ta SCO za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin da ma duniya baki daya. (Yahaya)