An karrama Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da lambar yabo, mako biyu bayan kammala aiki a Gwamnatin Muhammadu Buhari.
Fitacciyar tashar Talabijin ta Qausain TV ta mika lambar yabon ga tsohon ministan a yayin ziyarar da shugabannin tashar suka kai masa a gidansa dake Abuja.
A yayin ba da lambar yabon, Shugaban Tashar, Nasir Musa Albani Agege ya bayyana Isa Ali Pantami a matsayin wata kadara ta Nijeriya, wanda ya ce sun yi la’akari da cancanta ne zalla sakamakon namijin kokarin da tsohon ministan ya nuna wajen inganta bangaren Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani a lokacin da yake ofis.
Yana mai cewa, Pantami ya fidda Nijeriya kunya ta fuskar aiwatar da manyan tsare-tsaren wadanda suka dora kasar a tafarkin cigaba mai dorewa.
“Kazalika wannan lambar jinjina ce ga irin daruruwan cigaba da mai girma tsohon ministan ya samar a fannin sadarwar zamani da habaka tattalin arzikin zamani a Najeriya” In ji Albani.
A yayin da yake karbar lambar yabon, Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya gode wa Qausain TV bisa zakulo shi a bisa gudumawar da ya bayar a wannan fanni na sadarwar zamani.
Haka kuma ya yaba da irin jajircewar tashar ta Qausain TV wajen amfani da nagartattun kayan aiki da kuma sadaukarwa wajen ilmantar da al’ummar Najeriya da wajenta kusan shekara uku da suka gabata.
Ya ce “Hakika na san Qausain TV a matsayin tashar Talabijin da ke yada shirye-shiryenta a tauraron Dan Adam, wadda miliyoyin mutane ke kallonta, musamman saboda kyawawan shirye-shirye cikin harsunan Hausa, Turanci da kuma Larabci.”
“Kamar kuma yadda na san shi kansa shugaban tashar, wato Albani shekaru da yawa. Na san irin jajircewarsa wajen fasaha da kirkira. Shi ne ma Dan Nijeriya na farko da na sani wanda ya fara kirkirar Manhaja a kan Play Store da kuma Apple,” In ji Isa Pantami.
A daidai lokacin da yake taya Shugaban Qausain murnar wannan nasarar da ya samu cikin kankanin lokaci, sannan ya shawarci matasa da su yi koyi da shi domin cigaban kasarmu Najeriya.
Baya ga tawagar Qausain TV da suka bada lambar yabon, kwarkwaryar taron ya samu halartar Yan’uwa da abokan arziki na tsohon ministan a gidansa dake Abuja.