Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva da wasu kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland Chen Xu, ya bayyana ra’ayin kasar Sin dangane da batun kasar Sudan, a taro karo na 53 na kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD, wanda ya gudana jiya Litinin.
Chen Xu ya nuna cewa, duk da hali mai sarkakiyya da ake ciki a kasar Sudan, gwamnatin kasar tana dukufa wajen kiyaye hakkin dan Adam, tana kuma tsayawa kan hada kai da tsarin kiyaye hakkin dan Adam na MDD, lamarin da ya cancanci a yaba masa. To sai dai kuma ba za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Sudan ba, har sai al’ummar Sudan din sun ba da jagoranci, sun tafiyar da harkokinsu da kansu, sun kuma tsaya da kafafunsu, wajen lalubo hanyar daidaita batun kasar su bisa doka.
Chen ya kara da cewa, kasar Sin na mara wa kungiyar tarayyar Afirka AU, da sauran kungiyoyin kasa da kasa baya, wajen ci gaba da taka rawar da ta dace, kana ya kamata kwamitin kula da hakkin dan Adam shi ma ya goyi bayan wadannan kungiyoyi, wajen taka rawa mai amfani, da kauce wa barin lamarin ya kara ta’azzara.
Har ila yau, a cewar sa kafa kwamitin musamman na binciken kiyaye hakkin dan Adam a wasu kasashe, ba tare da amincewar su ba, ba zai yi amfani wajen kyautata halin da ake ciki a kasashen ba, kuma ba za a iya cimma burin da aka sanya gaba ba. (Tasallah Yuan)