Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele da aka dakatar ya garzaya babbar kotun birnin tarayya Abuja, yana kalubalantar tsare shi da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi.
A jawabinsa na farko kan sanarwa, Emefiele yana addu’ar kotu ta tabbatar masa da hakkinsa na walwala, saboda babu dalilin ci gaba da tsare shi.
- Kante Ya Yarda Ya Koma Saudiya Da Taka Leda
- Ranar Yaki Da Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Gurfanar Da Mutum 501 A Adamawa
Sai dai babban lauyan gwamnatin tarayya da kuma hukumar DSS sun dage cewa tsare Gwamnan CBN da aka dakatar yana kan ka’ida.
A wata karar farko da suka shigar kan karar da Emefiele ya gabatar, babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) da hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun shaidawa babbar kotun birnin tarayya cewa tsarewar ya samu goyon bayan umarnin wata kotun majistare.
Sun bayyana cewa kama tsohon gwamnan na CBN hukunci ne na hukumar DSS.
Har ila yau AGF na kalubalantar hurumin kotun da ya shigar da kara a gaban kotu, domin tun da farko bukatar da Mista Emefiele ya gabatar ya kamata kotu ta yi watsi da umarnin tsare shi maimakon neman a tabbatar masa da hakkinsa.
A nata bangaren hukumar ta DSS na kalubalantar kudirin neman belin da Mista Emefiele ya shigar.
An dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuli domin yanke hukunci.
A ranar 10 ga watan Yuni ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga ofishinsa na gwamnan babban bankin kasar.
Jim kadan bayan dakatar da shi hukumar DSS ta sanar da cewa Gwamnan babban bankin na CBN yana hannunta.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa dakatarwar ita ce ta ba da damar “bincike na ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi da na tattalin arzikin kasar nan.”