Hukumar Yaki da Sha da Hana Fataucin Miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta gurfanar da mutum 501 a kotu, bisa zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar Adamawa.
Shugaban hukumar a jihar, Femi Samson Agboala, ya sanar da haka a Yola, cikin bikin ranar na duniya, inda ya ce cikin mutum 501 akwai mata 10 da hukumar ta gurfanar gaban kotu.
- Arsenal Ta Taya Timber Yuro Miliyan 30
- Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Dokar Ta-Baci Kan Masu Kwacen Waya
Ya kara da cewa “NDLEA ta gurfanar da mutum 501, ta taimaka wa 357 sun samu lafiya, ta kame haramtattun kwayoyi kilogiram 1,164.700, daga watan Yunin 2022 zuwa Mayun 2023.
“Mun samar da Naira dubu 781,00, daga hannun wadanda kotu ta samu laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi, mun shigar ta asusun bai-daya na gwamnatin tarayya.
“Mun cafke mota kirar Corolla, babur mai kafa uku guda biyu, gidan kwana a garin Ngurore, a karamar hukumar Yola ta kudu, bayan mun gano kwayoyi masu nauyin kilogiram 250 an boye su cikin gidan” in ji Agboala.
Da yake jawabi a bikin, gwamnan Jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce gwamnatisa na goyon bayan da tallafawa duk wani shirin yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Gwamnan wanda mataimakiyarsa, Farfesa Kaletapwa G. Farauta ta wakilta, ya kuma shawarci iyayen yara da su rika sa ido da lura da sha’anin yaransu a kowane lokaci.
Ya ce hakan zai taimaka wajen kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Ya kuma roki malaman Addini da sarakunan gargajiya da su bada tasu gudumuwar ta hanyar fadakar da matasa illar ta’ammali da miyagun kwayoyi, wanda ya ce hakan zai rage yaduwar haramtattun kwayoyin a cikin jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp