Akalla mutane 15 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wasu sabbin hare-hare da aka kai a kauyukan Bwai da Chisu na karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.
LEADERSHIP ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata lokacin da mazauna garin suka kwanta barci.
Bincike ya nuna cewa maharan sun afkawa al’ummomin biyu lokaci guda inda suka kashe mutane tare da kone gidaje.
Wani shaidan gani da ido, Bamshak Ishaya ya yi zargin cewa ‘yan bindigar Fulani ne suka kashe wasu mutane a gidan wani shugaban al’umma a kauyen Chisu a daren ranar Talata da misalin karfe 11:00 na dare.
An gano cewa an kuma kone Cocin COCIN RCC da ke Bwai da ke kan hanyar Mangu zuwa Bokkos tare da kone gidaje da motoci da babura masu kafa uku.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, al’ummar yankin sun ji karar harbe-harbe, inda suka garzaya zuwa gidan Jagoran unguwarsu, don neman mafaka.
A Bwai, baya ga Cocin, an kuma kone gidaje da ke kusa da kasuwar, sannan an kone wata mata a yankin.
A halin da ake ciki, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Mangu ta kudu a majalisar dokokin jihar, Mista Bala Fwangje shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, “da misalin karfe 11 na dare, mun samu waya cewa makiyaya sun shigo Chisu da Bwai, da safiyar yau ne muka ji an kashe kimanin mutane 15, an lalata gidaje, an kone dukiyoyi da dama, har yanzu ban samu cikakken bayani ba.”
Haka zalika, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Mangu, Mista Markus Artu, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa lamarin ya faru amma har yanzu ba shi da cikakken bayani.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, DSP Afred Alabo ba mu samu jin ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.