‘Yansanda a jihar Ondo sun cafke wasu ma’aikatan Asibiti uku ciki har da wata mataimakiyar aikin jinya da kuma mai gadi da ke aiki a wata cibiyar kiwon lafiya garin Emure-IIe da ke a karamar hukumar Owo bisa zarginsu da da sanadin bacewar mahaifar wata jaririya.
Mahaifin jaririyar mai suna Tunde Ijanusi wanda ya bayyana kaduwarsa kan sakacin ma’aikatan Asibtin wajen bacewar, ya ce “ma’aikatan suna wasa da aikin su”.
Kakar jaririyar mai suna Funmilayo Ijanusi, ta sanar da cewa, ma’aikatan sun bayyana cewa, Kare ne ya shigo Asibtin ya sace mahaifar jaririyar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar SP Funmilayo Odunlami-Omisanya ta bayyana cewa, rundunar ta kama mutum uku bayan da mahaifin jaririya dan shekara 23 ya shigar da korafi a caji ofis na ‘yansanda da ke Emure-Ile.
Odunlami ya kara da cewa, mahaifiyar jaririyar‘yar shekara 19 ta haifi jariyar ce a ranar 15 ga watan Yuni a Asibin.
A cewar Odunlami, bayan da mahaifin jaririyar ya bukaci mahaifar jaririyar ne, sai malamar jinyar da mataimakiyarta suka gaza fito masu da mahaifar, inda ta kara da cewa, ‘yansandan sun gayyaci ma’aikatan aikin Asibitin biyu da maigadin Asibitin, inda ake ci gaba da gudanar da bincike a caji ofis din a Emure-Ile.