ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Li Qiang: Kamata Ya Yi Sin Da Jamus Su Kafa Wani Misali Na Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Turai

by CMG Hausa
3 years ago
Li Qiang

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce ya kamata kasashen Sin da Jamus su yi aiki tare, wajen zurfafa hadin gwiwar raya tattalin arziki da fasahohi, ta yadda hakan zai zama wani misali, da jagoranci, a fannin karfafa hadin gwiwar cimma moriya tare tsakanin Sin da Turai, da ingiza ci gaban duniya.

Firaminista Li Qiang ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin da yake halartar taron raya hadin gwiwar tattalin arziki da fasahohi tsakanin Sin da Jamus, karo na 11 a kasar Jamus.

  • Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Hakuri Kan Yadda Harkokin Siyasa Ke Gudana A Sudan Ta Kudu

Li ya kara da cewa, a wannan gaba da ake fuskantar sauye sauye, da rashin tabbas a duniya, karfafa hadin gwiwa zai taimakawa wajen cimma moriyar juna, da samar da kyakkyawan sakamako ga kowa, kana matakin shi ne ya dace a kara maida hankali a kansa.

ADVERTISEMENT

Daga nan sai ya jaddada wajibcin mayar da batun hadin gwiwar raya tattalin arziki da fasahohi tsakanin sassan biyu, a matsayin muhimmin jigo na hadin gwiwar kasa da kasa, da rungumar matakan dunkulewar tattalin arzikin duniya, da goyon bayan cinikayya maras shinge, da bunkasa matakan cin gajiya tare, da habaka ci gaban bil adama.

A nasa bangare, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, cewa ya yi kasar ba za ta amince da manufofin raba kan kasashen duniya ba, za ta kuma nacewa aiwatar da matakai a bude, tare da karfafa hadin gwiwa tare da Sin, da gaggauta bunkasa hadin gwiwar sassan kasa da kasa bayan annobar COVID-19.

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai

Scholz ya ce, Jamus a shirye take ta yi tukuru, wajen warware matsalolin hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, da gudanar da shawarwari tare da bangaren Sin. (Saminu Alhassan)

Li Qiang
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE
Daga Birnin Sin

Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE

November 7, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai

November 7, 2026
Wakilan Sin Da Amurka Sun Tattauna Kan Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Amurka Sun Tattauna Kan Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya

November 7, 2026
Next Post
An Dakatar Da Mourinho Wasanni 4 Kan Fada Da Alkalin Wasa

An Dakatar Da Mourinho Wasanni 4 Kan Fada Da Alkalin Wasa

LABARAI MASU NASABA

Messi Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare Ta MLS A Karo Na Biyu A Jere

Messi Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare Ta MLS A Karo Na Biyu A Jere

November 8, 2026
Hanyoyin Kare Fata Daga Illar Hasken Rana

Hanyoyin Kare Fata Daga Illar Hasken Rana

November 8, 2026
 Shin Tauraruwar Rarara Ta Fara Dusashewa?

 Shin Tauraruwar Rarara Ta Fara Dusashewa?

November 8, 2026
Jerin Sabbin Jarumai Matan Kannywood Takwas Da Za Su Ja Zarensu A 2027

Jerin Sabbin Jarumai Matan Kannywood Takwas Da Za Su Ja Zarensu A 2027

November 8, 2026
Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku

Sabon Hukuncin Kotu Kan ADC Na Iya Janyo Yaƙin Basasa — Amaechi

November 8, 2026
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira

Zaɓen 2027 Zai Fayyace Makomar Matasa — Tinubu

November 8, 2026
Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle

Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle

November 7, 2026
Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE

Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE

November 7, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai

November 7, 2026
Ku Karɓi Kuɗin APC, Amma Ku Fatattake Su A 2027, Makinde Ya Buƙaci ’Yan Nijeriya

Ku Karɓi Kuɗin APC, Amma Ku Fatattake Su A 2027, Makinde Ya Buƙaci ’Yan Nijeriya

November 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.