‘Yan bindiga sun kai hari yankin Ejule da ke karamar hukumar Ofu a Jihar Kogi, inda suka hallaka mutane da dama.
Rahotannin sun ce, an kai harin ne da misalin karfe 3 na daren yau Alhamis, inda suka hallaka wani fitattcen dan kasuwa da matarsa da kuma wani shugaban matasa.
- An Bayyana Ranar Buga El Clasico Tsakanin Real Madrid Da Barcelona
- Ba Zamu Lamunci Salwantar Rayuka Da Dukiyoyi A Katsina Ba -Gwamna Radda
An ruwaito cewa, albarushin ‘yan bindigar ya samu dan acabar ne, a yayin da matar albarushin ya same ta bayan ta fito tana neman mijin nata, inda suka mutu a nan take.
Wani mazauni yankin ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kuma bankawa wani gida wuta.
Mazaunin yankin wanda ya bayyan hakan a hirar da aka yi da shi ta wayar tafi da gidanka ya ce,“ ba mu san yawan adadin wadanda ‘yan bindigar suka hallaka a yanzu ba, amma an gano cewa, sun kashe dan acaba da matarsa da kuma shugaban matasa. “
“ Har yanzu akwai fargaba a yankin an kuma ga wasu gawarwaki da dama akan tituna kuma babu wanda zai iya zuwa wajen a yanzu.”
A wata hira da aka yi da mai bai wa gwamnan jihar shawara kan tsaro, Jerry Omadara (mai ritaya), ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai ya bayyana cewa, ba samu cikakken bayanai kan kai harin ba.
Rundunar ‘yansadan jihar ba ta fitar da wata sanarwar kan kai harin ba.