• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karuwar Nuna Wariya Alama Ce Ta Koma Bayan Kare Hakkin Bil Adama

by CMG Hausa
2 years ago
People hold signs saying "Say Their Names" and pay tribute to George Floyd and other Black lives lost to police brutality on the three-year anniversary of George Floyd's death at the Say Their Names Cemetery, Thursday, May 25, 2023, in Minneapolis. The murder of Floyd at the hands of Minneapolis police, and the fervent protests that erupted around the world in response, looked to many observers like the catalyst needed for a nationwide reckoning on racism in policing. (AP Photo/Abbie Parr)

Batun kare hakkin bil adama tsakanin manyan kasashe masu karfin fada aji, na cikin muhimman batutuwa dake jan hankali masharhanta a sassan duniya daban daban.

Ko shakka ba bu, ba wata alumma da ba ta fatan samun cikakkiyar kariya a fannonin hakkin bil adama daban daban, musamman a wannan lokaci da duniya ke samun ci gaba, da dunkulewa, ake kuma burin ganin dan adam ya yi rayuwa mai yalwa da walwala.

  • Sin Ta Yi Kira Da A Goyi Bayan CAR A Yunkurinta Na Shimfida Zaman Lafiya

To sai dai kuma wani abun lura a nan shi ne, yadda alummu daban daban ke kallon maanar kare hakkin bil adama, inda yayin da wasu ke kallon batun a matsayin wata manufa samar da ci gaba, da walwala, da gina alummar dan adam mai kyakkyawar makoma, wasu kuwa na amfani da batun kare hakkin bil adama ne a matsayin hanyar cin gajiyar siyasa, da nuna cewa su ne mafiya kwarewa a wannan fage.

Ga misali, a nan kasar Sin, akidar kare hakkin bil adama na nufin kare rayuka da walwalar alumma, da wanzar da zaman lafiya da ci gaban zamantakewar daukacin alummar kasa, da zamanantar da kasa daga dukkanin fannoni.

Kuma Sin ta amince cewa ba wata hanya dala tilo da za a ce ita ce kadai wadda bil adama zai bi wajen tabbatar da kare hakkokin bil adama, illa dai kawai ko wace kasa, ko yanki ya yi amfani da yanayin da yake ciki, wajen cimma nasarar kare hakkin alummar sa.

LABARAI MASU NASABA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

A daya bangaren kuwa, kasashen yamma, musamman Amurka, na kallon kan ta a matsayin mafi kwarewa, wadda kuma ta cancanci ta koyar da duniya yadda ake kare hakkokin dan adam, har ma a wasu lokutan yan siyasar ta ke nuna yatsa ga sauran sassa, kan yadda suke aiwatar da na su manufofin na kare hakkin bil adama.

To amma Bahaushe kan ce Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo, wato dai ko wace kasa, ita ta fi sanin yanayi mafi dacewa na matakan da za ta iya aiwatarwa domin kare alummar ta daga fadawa rikici, ko gurguncewar hakkin alummar ta.

Kaza lika, a yayin da Amurka ke sukar sauran sassa da gazawa wajen kare hakkokin alumma, kamata ya yi ta fara duba matsalolin ta na cikin gida, kamar batun nuna wariyar launin fata da ya zama ruwan dare a kasar.

Masharhanta na cewa, alamar ci gaban alumma na bayyana ne daga imanin alumma da makomar su.

Wani sharhi da jaridar Washington Post ta wallafa a baya bayan, ya nuna sakamakon wani bincike da aka gudanar game da wariyar launin fata a Amurka, wanda ya tabbatar da cewa, kaso mafi rinjaye na Amurkawa masu asali daga Afirka sun damu, da yadda ake samun karuwar nuna wariyar launin fata gare su a shekarun baya bayan nan, sama da yadda abun yake a baya.

Kaza lika, sakamakon binciken ya nuna rashin gamsuwa da wannan rukuni na alummar Amurka ke da shi don gane da kyautatuwar yanayin kare hakkokin su, ciki har da na zamantakewa, da rashin daidaito a fannin tattalin arziki, da kula da lafiya, da batun fuskantar hare haren bindiga da dai sauran su.

Idan mun yi laakari da sakamakon wannan bincike, za mu iya gano cewa, Amurka na da na ta manyan matsaloli na kare hakkin dan adam, wadanda ya kamata ta tunkara, maimakon mayar da hankali ga sukar yadda wasu kasashen na daban ke kokari karewa alummun su hakkoki. Idan kuwa Amurka ba ta dauki wannan mataki ba, to sakamakon da za ta ci gaba da samu a cikin gida, zai dada tabbatar da kallon da wasu masu fashin baki ke mata, na mai take laifin ta domin hangen na wasu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
Daga Birnin Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Next Post
Shari’ar Zaɓe: Gwamnan Sokoto Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Jihar

Shari'ar Zaɓe: Gwamnan Sokoto Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Jihar

LABARAI MASU NASABA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.