Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa ba za a rufe rajistar zaɓe ba har sai hukumar ta gamsu da cewa jama’a sun yi amfani da damar ƙarin wa’adin da za ta yi, sun yi rajista sosai.
Yakubu ya ce saboda haka mutane su kwantar da hankalin su, INEC ba za ta rufe yin rajistar zaɓe ba a ranar 30 ga Yuni, 2022.
Shugaban ya yi wannan albishir ne yayin da ya ke wa dandazon matasa jawabi a Tsohon Dandalin Fareti a Abuja.
Matasan dai sun taru ne domin halartar gangamin wayar wa da matasa kai kan muhimmancin yin rajista.
INEC ce ta shirya gangamin tare da haɗin-gwiwar ƙungiyar bin diddigin zaɓe ta ‘Yiaga Africa’, kuma Ƙungiyar Tarayyar Turai ce ta ɗauki nauyin shirya taron.
A jawabin sa da ya ke yi a ranar Asabar, Yakubu ya ce, “Ku na so ku sani ko INEC za ta rufe yin rajista nan da kwanaki biyar? To a madadin INEC ina tabbatar maku da cewa ba za a rufe rajista ba har sai mun gamsu da cewa yawan jama’ar da mu ke son ganin sun mallaki rajistar zaɓe duk sun samu dama sun yi rajista.”
Yakubu ya ce nan ba da daɗewa ba INEC za ta fitar ranar da za daina rajista.
Yayin da ya ke ƙarin haske kan cigaban da ake samu wajen aikin rajista, ya ce a cikin kwana biyar cakal da ake rajista a cikin Tsohon Filin Fareti, an yi wa mutum fiye da 14,000 rajista.
A wani labarin makamancin wannan, Farfesa Yakubu ya jaddada cewa INEC za ta ƙara yawan na’urorin rajistar zaɓe a dukkan jihohin ƙasar nan.
Ya ce INEC za ta ƙara wa’adin yin rajista domin tabbatar da cewa ta bai wa ɗimbin ‘yan Nijeriya isasshen lokacin yin rajista, ta yadda jama’a da dama za su samu jefa ƙuri’a a zaɓen 2023.
Ya ce: “Mun raba ƙarin na’urorin yin rajista zuwa jihohi a wannan makon, kuma yanzu ma za a ƙara aikawa da su a wasu wuraren tsakanin Litinin zuwa Juma’a.”
Lokacin da ya ke amsa jinjinar da dandazon matasa su ka riƙa yi, su na cewa, “Ba ma son maguɗin zaɓe”, Yakubu ya tabbatar masu da cewa, “Zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka yi a makon jiya ya yi kyau. Na gwamnan Jihar Osun da za a yi nan gaba zai fi na Osun kyau. Shi kuma zaɓen 2023 zai fi kowane sahihanci.”
A jawabin sa, Jakaden Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Samuel Isipi, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da kada su riƙa sayar da ƙuri’un su ga ‘yan siyasa.