A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi kokarin yin ceto yadda ya kamata, da samar da jiyya ga mutanen da suka jikkata, tare da inganta matakan tsaro, bayan fashewar wani abu a gidan cin abinci a jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Shugaba Xi ya kuma bukaci a yi kokarin gaggauta gano musabbabin hadarin tare da hukunta wadanda ke da hannu kamar yadda doka ta tanada.
Ya kara da cewa, ya kamata dukkan yankuna da sassan da ke da alaka su gudanar da bincike tare da gyara dukkan nau’o’in hadurra daka iya faruwa ba zato ba tsammani
A bisa umarnin Xi, an aike da wani rukuni na aiki da ya kunshi sassa da dama na gwamnatin tsakiya zuwa wurin da abin ya faru domin jagorantar ayyukan ceto.
Mahukuntan jihar ta Ningxia sun sanar da cewa, fashewar da ta auku a wani gidan cin abinci a Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia, a daren ranar Laraba, ta yi sanadiyar mutuwar mutane 31 tare da jikkata wasu 7. (Ibrahim)